Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Thursday, April 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZa a yi sallar kisfewar rana yau Talata a Saudiyya

Za a yi sallar kisfewar rana yau Talata a Saudiyya

Date:

Hukumomin Saudiyya sun ce za a gabatar da Sallar Kisfewar Rana a Masallacin Harami yau Talata.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da shafin Facebook na Haramain Sharifain ya wallafa ranar Litinin.

 

Tun a makon da ya gabata, aka samu rahoton za a samu kisfewar rana a wasu ƙasashen duniya ciki har da Saudiyya.

 

“Wanda zai jagoranci Sallar Kisfewar Rana a Masallacin Harami a yau (Talata) shi ne Sheikh Bandar Baleelah.

 

Yayin da Sheikh Ahmad Huzaify zai jagoranci Sallar a Masallacin Madina.

 

Za a gudanar da Sallar ne da misalin karfe 1:45 na rana dai DAI da 4:45 agogon Najeriya.

 

Musulunci ya sunnanta cewa duk lokacin da aka samu kisfewar rana ko wata to Musulmi su yi sallar nafila da nufin neman sauki daga Ubangiji Madaukakin Sarki.

 

A wani hadisi, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya ce: “Haƙiƙa rana da wata ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah. Ba sa kisfewa saboda mutuwar wani ko saboda rayuwarsa”.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...