ALA ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.

 

Idan dai ba a manta ba, an samu ɓaraka tsakanin Rarara da gwamnatin jihar Kano, inda mawaƙin ya daina yi wa Gandujiyya waƙoƙin siyasa.

 

A maimakon haka, sai aka jiyo shi yana yi wa ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADP, Sha’aban Sharaɗa waƙa.

 

“Yaƙin kare mutuncin Dauda ya fi yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ɗan Majalisar Tarayya a gare ni.

 

“Mun yi mutunci da mutuncinka, ka yi mutunci da mutuncinmu shi ne babban arziƙi na zaman tare.

 

“Takarata fansa ce a wajen kare mutunci da haƙƙin Dauda”, in ji ALA.