Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNAFDAC ta gargadi al'umma kan yin amfani da maganin tarin da ya...

NAFDAC ta gargadi al’umma kan yin amfani da maganin tarin da ya kashe mutane a Gambia

Date:

Najeriya ta gargadi al’ummar kasar nan da su guji  amfani da wasu nau’ukan magungunan tari da ake alakanta su da sanadin mutuwar mutane da dama a Gambia.

Ana zargin magungunan iri hudu, na kamfanin hada magani na Maiden Pharmaceuticals da ke Indiya, sun gurbata ne da wasu abubuwa masu cutarwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gargadi kasashen duniya kan su yi hattara da magungunan na yara.

Yanzu haka hukumar kula da ingancin abinci da mugunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta bukaci al’ummar kasar da su kaurace wa magungunan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, NAFDAC ta ce duk wanda ya san ya yi amfani da wani daga cikin irin wadannan magunguna, kuma ya ji wasu alamomi da bai gane ba a tare da shi, to ya garzaya ya sanar da hukumomin lafiya.

Hukumar ta kara da cewa wasu daga cikin cututtukan da magungunan ke haifarwa sun hada da ciwon ciki, da amai, da gudawa, da gaza yin fitsari, da ciwon kai, da lalurar koda mai tsanani wadda ka iya sanadin mutuwa.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace ko akwai magungunan a kasuwannin Najeriya ba.

Magungunan tarin dai su ne na ‘Promethazine Oral Solution’, da ‘Kofexmalin Baby Cough Syrup’, da ‘Makoff Baby Cough Syrup’ da kuma ‘Magrip N Cold Syrup’.

A wata sanarwa da kamfanin magungunan ya fitar, ta ce ya yi takaicin matsalolin da magungunan suka haifar.

Kamfanin ya kara da cewa ya bi duk wasu ka’idojin da aka gindaya na hada magani a kasar Indiya, kuma yana bayar da hadin kai a binciken da ake gudanarwa.

Tuni dai Gambia ta fara janye magungunan daga kasuwanninta.

Ana alakanta magungunan tarin da yin sanadin mutuwar akalla yara 69.

Kuma hukumar lafiya ta nuna fargabar cewa ba a Gambia kawai ake amfani da magungunan ba.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...