Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaWHO ta kaddamar da shirin dakile kashe Kai a Afrika

WHO ta kaddamar da shirin dakile kashe Kai a Afrika

Date:

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kaddamar da wani shirin wayar da kan Al’umma da kuma daukar matakan dakile kashe kai a Najeriya da sauran yankunan Afirka.

 

A cewar hukumar, kusan mutane 11 a cikin 100,000 a kowace shekara suna mutuwa ta hanyar kashe kansu a yankin Afirka, wanda ya zarce adadin kowane yanki a fadin duniya.

 

Wannan ya biyo bayan rashin isassun matakan magance da kuma hana abubuwan da kan ingiza mutum ya kashe Kansa.

 

Wadanda suka hada da, matsin rayuwar, tsananin damuwa da kuma matsalar kwakwalwa wanda a halin yanzu ya shafi mutane miliyan 116, a cewar wata sanarwar da WHO ta fitar.

 

Sakamakon haka, gabanin ranar kiwon lafiyar kwakwalwa ta duniya a ranar 10 ga watan Oktoba, WHO ta kaddamar da wani kamfen a kafafen sada zumunta da nufin isar da wannan manufa ga mutane miliyan 10 a fadin Afrika.

 

Kamfen din zai wayar da kan alumma hadi da neman goyon bayan gwamnatoci da masu tsara manufofi don kara mayar da hankali da ware kudaden da za’a gabatar da shirye-shiryen kula da lafiyar kwakwalwa domin dakile kashe kai tsakanin Al’umma.

 

Daga cikin manufofin da ake yunkurin samarwa sun hada da; samar da ma’aikatan kiwon lafiya don tallafawa masu fama da tunanin kashe kansu da kuma ilimantar da mutanen da za su fuskanci wadannan tunanin akan inda za su je domin neman taimako.

Latest stories

Related stories