Saurari premier Radio
27.6 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabu abinda zai wargaza kasar nan-IBB

Babu abinda zai wargaza kasar nan-IBB

Date:

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce babu abin da zai wargaza kasar man duk da irin matsalolin da take fuskanta.

 

Dangane da bikin cikar Najeriya shekaru 62 da samun ’yanci da za a yi a ranar Asabar, Janar Babangida ya yi wannan jawabi ne yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin Jihar Neja.

 

Tsohon Shugaban Kasar ya shawarci al’ummar Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu kwarin gwiwa da yi wa kasar kyakkyawan fata, yana mai mai cewa kasar za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

 

Sai dai Janar Babangida ya ce hakan ba zai tabbata ba sai an samu hadin kan ’yan kasa musamman matasa, inda ya bukaci kowa ya kara himma.

Ya yi kira ga matasa a kan kada su bari ’yan siyasa su ribaci kuruciyarsu wajen amfani da su a matsayin karnukan zabe yayin da Babban Zaben kasar ya gabato.

 

Ya yaba wa kokarin gwamnatoci daban-daban a Najeriya wajen ganin kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya, ya kuma yi kira don samun karin nasarori.

 

Ya ce burinsa shi ne ya ga Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki da hadin kai ta yadda zaman lafiya zai zarce komai.

 

Ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa nan ba da jimawa ba za a warware tankiyar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...