Saurari premier Radio
26.6 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJam'ian tsaro sunyi kadan a Najeriya-Abdussalam

Jam’ian tsaro sunyi kadan a Najeriya-Abdussalam

Date:

Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun yi kadan a kasar nan.

 

A cewarsa wannan ne ya sa aka Gazan magance matsalar tsaro da ake fuskanta a yanzu.

 

Janar Abdulsalami ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin ganawa da manema labarai a gidansa da ke Minna, babban birnin Jihar Neja.

 

Ya yi kira da a dauki karin jami’an tsaro domin kawo karshen ta’addancin da ya dabaibaye kasar.

 

A cewarsa, daukar karin jami’an tsaron yana da muhimmanci la’akari da yadda wadanda ake da su a yanzu suke matukar shan wahala da hakan zai kawo nakasu wajen inganta ayyukansu.

 

Ya kuma jaddada bukatar samar da ingantattun kayan aiki ga jami’an tsaro domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da kuma tabbatar da isasshen tsaro da aminci.

 

Tsohon Shugaban Kasar ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da ba da gudunmuwa ta hanyar mika duk wani rahoto da zai taimaka a inganta al’amuran tsaro a kasar.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories