Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNa rungumi kaddara ba zan daukaka kara ba – Ahmed Lawan

Na rungumi kaddara ba zan daukaka kara ba – Ahmed Lawan

Date:

Na rungumi kaddara ba zan daukaka kara ba – Ahmed Lawan

 

Shugaban majalisar dattijai sanata Ahmed Lawan ya ce rungumi kaddara gameda hukuncin kotu da ya tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halastaccen dan takaran sanata mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa a zaben shekarar 2023.

 

A jiya labara ne dai wata babbar kotun tarayya dake da zama a Damaturu ta yanke hukuncin kan kowa zai yiwa jam’iyyar APC takaran sanata a mazabar Yobe ta Arewa.

 

Ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter sanata Ahmad Lawan ya kuma yabawa gwamna Mai Mala Buni sakamakon shugaban ci na gari da ya ce yana yiwa jam’iyyar APC a jihar Yobe.

 

Manyan yan sitasa na zawarcin Sanata Shekarau daga NNPP.

 

Shugaban majalisar dattijan ya kara da cewa bayan hukuncin kotun ya tuntubi abokan siyasar sa kan mataki na gaba kuma duk bakinsu yazo daya cewa kar a daukaka kara.

 

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories