27.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiManyan yan siyasa na zawarcin Sanata Shekarau daga NNPP.

Manyan yan siyasa na zawarcin Sanata Shekarau daga NNPP.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

 

Tsohon gwamnan Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya labarin dake cewar zai kara sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP.

 

Mai Magana da yawun Sanata Shekarau Sule Ya’u Sule ya tabbatar da haka a tattaunawarsa da manema labarai, inda ya musanta batun da wasu kafafen yada labarai suka fitar dake cewar Shekarau na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP.

 

Sai dai Sule Yau Sule ya tabbatar da cewar manyan ‘yan siyasa a kasar nan na zawarcin Sanata Shekarau domin ganin ya koma jam’iyyunsu, ko da yake ba shi da niyyar yin haka.

 

Yace batun da ake yadawa na ficewar Shekarau daga NNPP baya rasa nasaba da rashin cika alkawari na yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarensu dana tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

 

To sai dai tun bayan da aka wayi gari da wannan tirka tirki jamiyyar NNPP mai alamar kayan marmari batace komai ba kan batun

Latest stories