Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDole jam'iyun siyasa su sanya mata da matasa cikin kwamitinsu na neman...

Dole jam’iyun siyasa su sanya mata da matasa cikin kwamitinsu na neman zaɓe – CITAD

Date:

Shehu Usman Salihu

 

Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD, tayi kira ga jam’iyyun siyasa a ƙasar nan, su sanya mata da matasa cikin kwamitinsu na neman zaɓe a kowane mataki.

 

Babban jami’in cibiyar, Malam Isah Garba ne yayi kiran yayin wani gangamin taron mata da matasa karkashin shirinsu na shigar mata da matasa harkokin siyasa, da ya gudana da safiyar litinin ɗin nan a Kano

 

Wannan dai ɓangare ne na ranar matasa ta duniya da akai bikinta a juma’ar da ta gabata.

 

Isa Garba ya ce, mata da matasa ne kaso mafi yawa cikin al’umma, sai dai an barsu a baya ta fannin shugabanci a ƙasar nan, alhali suna da gudun mawar da zasu iya bayarwa wajen gyara al’amura.

 

Jami’in ya kara da cewa sun san lokaci ya kure na fitar da ƴan takara a jam’iyu, amma lokaci bai kure ba wajen sanya mata da matasa cikin kwamitin neman zaɓen dan takara ta yadda duk abin da za’a tattauna ra’ayinsu zai shiga.

 

Ko wace shekara dai, majalisar ɗinkin duniya kan fitar da take domin yin bikin ranar matasan, taken na wannan shekarar shi ne “bada goyon baya ga matasa”.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...