Mukhtar Yahya Usman
Gwamnonin jihohi kasar nan 36 za su gidanar da wani muhimmn taro a ranar Laraba a Abuja domin tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da matsalolin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar al’ummar kasar.
Daraktan yada labaran gwamnonin kasar nan Abdulrazak Bello-Barkindo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Ya ce ana sa ran batu kan halin da tattalin arziki kasar nan ke ciki zai mamaye kaso mafi yawa na abubuwan da za a tattauna a taron.
Barkindo yace ba gaskiya ba ne, rahotannin da wasu kafafen yada labarai a ke yadawa cewa gwamnonin sun bai wa shugaban kasa shawara da ya tilasta wa ma’aikatan gwamnati masu shekaru 50 zuwa sama ritayar dole.
A cewarsa, taron zai kasance na farko a wannan Shekarar ta 2022 da gwamnonin za su yi tare a kan tattalin arzikin kasa.
Bello-Barkindo ya ce gwamnonin za su kaddamar da asusun kula da lafiya a matakin farko da kuma tsarin bankin duniya SFTAS kafin su shiga taron, wanda ake sa ran za a fara da karfe biyu na rana.
A cewarsa gwamnonin za Kuma su sami sabbin bayanai game da shirin farfado da tattalin Arzikin Kasa bayan cutar Covid19