33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGanduje ya aike da karin mutum guda da zai nada Kwamishina gaban...

Ganduje ya aike da karin mutum guda da zai nada Kwamishina gaban majalisa don tantancewa

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya tura da karin sunan mutum daya da majalisar dokokin Kano zata tantance a matsayin wadanda za a nada kwamishinoni.

 

Majalisar ta karbi sunan karin mutum dayan Dakta Ali Musa Burum Burum, a yau Talata.

 

A ranar Litinin data gabata ne gwamna Ganduje ya aikewa da majalisar sunayen mutane takwas da za a tantance tare da amincewa a nada su kwamishinoni a ma’aikatu daban daban.

 

Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da wasu kwamishinonin sukayi don tsayawa takara a matakai daban daban a zaben badi dake tafe.

Ya zuwa yanzu dai mutane tara ake sa ran majalisar dokokin zata tantance a ranar Litinin mai zuwa.

Latest stories