Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBani da buri da ya wuce hidimtawa yan Najeriya –Atiku

Bani da buri da ya wuce hidimtawa yan Najeriya –Atiku

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba shi da wani buri face yi wa al’ummar kasar nan hidima.

 

Ya bayyana hakan a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa a wani taro da magoya bayan jam’iyyar APC suka koma PDP.

 

Atiku Abubakar, wanda gungun jama’a suka tarba a dandalin Mahmud Ribado da ke Yola, ya ce zai magance kalubalen da kasa ke fuskanta idan aka zabe shi.

 

Wannan dai shi ne karon farko da ya ziyarci mahaifarsa tun bayan samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

 

A yayin ziyarar dai Atiku ya bukaci al’ummar jihar Adamawa su hada kai, tare da ci gaba da goyon bayan da suke ba shi tsawon shekara talatin da ya shafe yana siyasa.

 

Ya kuma yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar su hada kai, su yi aiki tare domin samun nasara a zaben badi.

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...