31.9 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiKiwon LafiyaBuhari ya nada Dangote shugaban kwamitin dakile cutar malaria na kasa.

Buhari ya nada Dangote shugaban kwamitin dakile cutar malaria na kasa.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada  Alhaji Aliko Dangote a matsayin shugaban kwamitin dakile cutar zazzabin cizon sauro na kasa wato malaria.

 

Rahotanni na cewar Buhari ya nada Dangote ne saboda gudummuwar da yake bayarwa a bangaren lafiya a nahiyar Afirka bakidaya.

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kwamitin mai mutane 16 a ranar Talata, inda ya ce nasararsu a aiwatar da shirin za ta taimaka wajen rage kudin da cutar ke lakumewa daga tattalin arzikin kasa.

 

Kudin da aka kashewa kan cutar malaria ya kai Naira milyan dubu 687 a bana.

 

Shugaban ya kuma sanar da kwamitin cewa baya ga inganta lafiya, shirin zai amfani zamantakewa da tattalin arzikin kasar nan.

Latest stories