Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn sake sanya dokar hana hawa Babura a jihar Zamfara

An sake sanya dokar hana hawa Babura a jihar Zamfara

Date:

Karibullah Abdulhamd Namadobi

 

Gwamnatin Zamfara ta sake kafa dokar hana hawa babur a wasu unguwanni da garuruwa da ke fadin jihar.

 

Gwamnan jihar, Bello Matawalle ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnati da ke Gisau.

 

Matawalle yace saboda ganin yadda ‘yan bindiga suka mamaye wasu yankunan Gusau, ya sa aka dauki matakin hana hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a Gusau.

 

Cikin wuraren da aka lissafa, har da Mareri, da Damba, da Tsunami, da Tsauni, da Barakallahu, da Samaru, sai Gada Biyu, da Janyau ta Gabas.

 

Gwamnati ta kuma umarci jami’an tsaro su bindige duk wanda suka gani a kan babur tsakanin wannan lokaci a wajen Gusau idan ya ki tsayawa lokacin da suka umarce shi ya tsaya.

 

 

Gwamna Matawalle ya ce, daga yanzu duk wani bako da ya nemi masauki a kowane Otal dole ne ya gabatar da ingantaccen katin shaida.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories