33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBabu wata matsala tsakanina da Shekarau- Kwankwaso

Babu wata matsala tsakanina da Shekarau- Kwankwaso

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon gwaman Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce Babu wata matsala ko barakar siyawa tsakaninsa da Malam Ibrahim Shekaru.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a zantawarsa da BBC ranar Laraba.

Ya ce rahotannin da ake yadawa game da rashin jituwa tsakaninsa da Shekarau ba gaskiya ba ne.

Wannan na zuwa ne bayan da labari ya karade kafafan sada zumunta cewa Shekaru zai fice daga NNPP saboda rashin Adalci.

Sai dai Kwankwaso ya ce ko da yake shi ma ya samu wannan labari amma ba haka batun ya ke ba.

2023: Kwankwaso zai kaddamar da Pastor a matsayin mataimakinsa

Manyan yan siyasa na zawarcin Sanata Shekarau daga NNPP.

“Gaskiya babu wata yarjejeniya da aka yi da ta wuce akwai bukatu da aka kawo kuma mun yi kokarin biyansu amma ba a kawo su a kan lokaci ba.

‘Kuma babu yadda za mu iya yi musamman abin da ya shafi takara,” in ji tsohon gwamnan na Kano.

Kwankwaso ya ce galibin wadanda Shekarau ya kawo domin yin takara a NNPP a kurarren lokacin suka zo.

Ya kara da cewa INEC ba za ta amince da takararsu ba domin an kammala zabukan fitar da gwani.

Sai dai ya ce idan aka kafa gwamnati za su samu mukamai masu daraja.

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa hakan ba zai haifar da wata matsala a jam’iyyar NNPP ba.

Latest stories