Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIndependence: Buhari zai yiwa alummar kasa jawabi

Independence: Buhari zai yiwa alummar kasa jawabi

Date:

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa alummar kasar nan jawabi da safiyar ranar Asabar.

Wanann na zuwa ne a Wani bangare na bikin samun ‘yancin-kan Najeriya shekaru 62.

Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba.

Buhari zai gudanar da jawabi ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe yayin da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ‘yancin-kai daga Turawan Birtaniya.

“Ana umartar gidajen talabijin da rediyo da sauran kafofin labarai na latironi da su jona jawabin daga gidan talabijin na NTA da kuma Rediyo Najeriya,” a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar.

Tun daga farkon makon nan aka ga sojojin Najeriya na shirye-shiryen bikin na ranar Asabar, inda jiragen soja za su dinga wasa a sama da kuma faretin girmamawa.

Latest stories

Related stories