Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKoyar da dalibai da harshen Hausa zai magance matsalar ilimi a Kano-Munzali...

Koyar da dalibai da harshen Hausa zai magance matsalar ilimi a Kano-Munzali Jibril

Date:

 

Mukhtar Yahya Usman

 

Fitaccen masani kuma malamin Harshen Turanci Farfesa Munzali Jibril ya ce koyar da dalibai da harshen Hausa shi ne kadai mafita ga matsalar ilimi a Arewacin kasar nan.

 

Munzali Jibril ya bayyana hakan ne yayin taron wuni daya da ilahirin ‘yan takarar gwamna a mabanbantan jam’iyyu domin gabatar musu da manufofin da za su ciyar da Kano da Jigawa gaba.

 

Taron wanda Zauren Kwararru na Kano da Jigawa (Kano Jigawa Professional Forum) ya shirya da manufar kawo gyara kan yadda ake tafiyar da al’amura a jihohin biyu.

 

Farfesa Munzali ya ce dalibai da dama na da hazaka da za su iya karatu mai zurfi amma rashin kyakkyawan turanci na dakilesu.

 

Ya ce tunda dai karatun Firamare da na karamar sakandire na hannun gwamnatocin jihohi to ya kamata su sauya tsarin.

 

A cewarsa a yanzu dalibi zai gama makaranta ya kuma samu sakamako amma da za a sanyashi ya rubuta layi daya na turanci ba zai iyaba.

 

Adon haka ya ce zauren yana bada shawara ga masu ruwa da tsaki da su mayar da harshen uwa wanda za a dinga amfani dashi a makarantun firamare da na karamar sakandire.

 

Da yake nasa jawabin daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan Kano kuma mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ya ce matukar ya samu nasara to ba shakka zai yi amfani da shawarwarin da zauren ya bayar.

 

A cewarsa ba karamin tunani aka yi ba wajen fitar da tsare-tsaren da ake ganin za su ciyar da Kano gaba.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...