Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar direbobin Tifa a Kano ta rantsar da sabbin shugabaninta na rassa...

Kungiyar direbobin Tifa a Kano ta rantsar da sabbin shugabaninta na rassa 196

Date:

Kungiyar direbobin tifa ta kasa reshen jihar Kano, ta rantsar da sabbin shugabanin rassan kungiyar dake jihar nan.

 

Kungiyar da gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabanin nata na rassa su 196 wanda ya gudana a sakatariyar kungiyar dake nan Kano a Lahadin nan.

 

Ministan Sufuri ya baiwa kamfanin Dantata & Sawoe watanni 4 ya Kamala tintin Western bypass a Kano

 

Da yake jawabi shugaban kungiyar ‘yan tifa na jihar nan Mamunu Ibrahim Takai, ya bukaci sabbin shugabanin rassan dasu kasance masu kwatanta adalci wajen sauke nauyin dake kansu.

 

A nasa bangaren shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa na kasa reshen Kano da Jigawa da Bauchi Maude Nasir, ya ce suna da kyakkyawar alaka da direbobin tifa a jihar nan sabanin yadda ake samun kananan matsaloli daga wasu masu tsamo yashi.

 

Shima daya halarci gurin taron Wazirin Garin Malam, Abubakar Rabo Abdulkarim, ya yabawa uwar kungiyar ta direbobin Tifar bisa yadda suke tallafawa marasa galihu dake cikin su da kuma ‘yara marayu da iyayen su direbobi suka rasu.

 

Rabo Abdulkarim, ya kuma bukaci direbobin das u cigaba da bin doka da oda yayin da suke gudanar da ayyukan su na dibar yashi da kuma tuki a cikin gari.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...