Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMinistan Sufuri ya baiwa kamfanin Dantata & Sawoe watanni 4 ya Kamala...

Ministan Sufuri ya baiwa kamfanin Dantata & Sawoe watanni 4 ya Kamala tintin Western bypass a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Tarayya ta baiwa kamfanin Dantata & Sawoe wa’adin watanni hudu ya kammala aikin titin Western Bypass da ke birnin Kano.

Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub ne ya ba da wa’adin ranar Asabar, lokacin da yake duba aikin titin mai tsawon kilomita 26.6.

Ministan ya koka kan yadda aikin ke tafiyar hawainiya.

A cewarsa ya zama wajibi kamfanin ya kammala shi nan da karshen shekarar da muke ciki.

“A zahirin gaskiya wannan aikin yana tafiyar hawainiya. Saboda haka, na ba wannan kamfanin nan da karshen watan Disamba ya kammala shi.

“Dole ne a kammala wannan aikin kafin wa’adin gwamnatin Buhari ya kare.

“Za mu samar da dukkan kudaden da ake bukata ga aikin don tabbatar da ba mu bar kowanne aikin da muka fara ba kafin karewar wa’adin gwamnatinmu,” inji shi.

A nasa bangaren Injiniyan da ke kula da aikin, Kasimu Maigwandu, ya ce tashin farashin kayayyaki, musamman man dizal ne babban kalubalensu a aikin.

Sai dai ya ce tuni suka kammala kaso 71.18 cikin 100 na aikin, kuma suna da kwarin gwiwar kammala ragowar kafin wa’adin da aka ba su ya cika.

Titin dai ya faro ne tun daga Na’ibawa a kan hanyar Kano zuwa Zaria kuma ya kare a garin Dawanau da ke hanyar Kano zuwa Katsina.

An bayar da shi ne tun a shekarar 2007 bisa yarjejeniyar kammalawa cikin shekara uku.

Kafin daga bisani gwamnatin Buhari ta sabunta tare da kara wa’adin kwangilar.

Kazalika, Minista EL-Yakub ya duba aikin titin Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi, inda ya ce Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar jihohin Kano da Katsina, wadanda aikin ya shafa sun kammala yarjejeniyar biyan diyyar da take yi wa aikin tarnaki.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...