24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKiwon LafiyaWani mummunan hadari ya hallaka kusan mutum 10 a Abuja.

Wani mummunan hadari ya hallaka kusan mutum 10 a Abuja.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Wani mummunan hadarai da ya auku a Abuja babban birnin tarayya ya jikkata mutum goma tare da hallaka mutum tara.

 

Hadarin ya auku a Yangoji dake Abuja, inda ya rutsa da mutum 22 gaba dayansu maza.

 

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.

 

A cewar mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem hadarin ya auku a ranar Lahadin da ta gabata.

 

Kamfanin dilkancin labarai na kasa NAN ya rawaito cikin sanarwar cewa, hadarin ya rutsa da mota dauke da fasinjoji, wadda ta taso daga jihar Osun zuwa Katsina inda tayi taho mu gama da wata motar daukar kaya.

 

Masu ruwa da tsaki kan sha’anin sufuri dai kanyi kiraye-kiraye ga alumma don kaucewa tukin ganganci duba da yadda a yawan lokuta hakan ke haddasa mummunan hadari.

 

Baya ga tukin ganganci rashin kyawun hanya da rashin kula da lafiyar ababan hawa daga direbobi na cikin abinda ke haddasa hadari akan hanya, hakan kuma na jawo asarar rayuka da dukiya a sassan Najeriya.

Latest stories