37.6 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiHukumar NDLEA ta kama muggan yan ta'adda a jihar Ondo.

Hukumar NDLEA ta kama muggan yan ta’adda a jihar Ondo.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Hukumar nan mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta samu nasarar chafke wasu muggan yan ta’adda guda takwas.

 

Yan ta’addar sun fada komar NDLEA a wani daji dake jihar Ondo, inda ake zarginsu da garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da kuma fashi da makami.

 

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA Femi Babafemi ya fitar tace, sun sami bayanan sirri ne kan maboyar yan ta’addar kuma suka nausa cikin dajin dake karamar hukumar Akure ta jihar Ondo inda a nan ne sukayi nasarar chafke mutum takwas.

 

Bayan kama yan ta’addar an samesu da bindiggi da harsasai da babura da layu da kuma buhu sama da 20 na tabar wiwi, harma da wasu abubuwa masu fashewa.

 

Andai kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’ar data gabata..

Latest stories