Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNBC ta janye rufe wasu kafofin yada labarai a kasar nan

NBC ta janye rufe wasu kafofin yada labarai a kasar nan

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai ta kasa (NBC) ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu kafofin yada labarai saboda gaza sabunta lasisinsu.

Darakta Janar na Hukumar, Malam Balarabe Shehu Ilelah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a a Abuja.

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’a, 19 ga watan Agustan 2022 ne NBC ta sanar da kwace lasisin kafofin yada labarai sama da 50.

Cikinsu kuwa har da kafar sadarwa ta Kamfanin DAAR da Rhythm FM da gidan talabijin na Silverbird , saboda bashin da take bin su na sama da Naira biliyan 2.6.

Matakin ya jawo suka ga hukumar wadda a kwanan nan ta ci tarar kafar labarai ta Media Trust naira miliyan biyar da wasu kamfanonin tauraron dan Adam kan fim din da suka haska game da ‘yan fashin daji a Jihar Zamfara.

Ilelah ya ce ya samu kyakkyawan martani daga tashoshin yada labaran da ba su sabunta lasisin nasu ba, wanda ya hada da manyan kafofin yada labarai cikin kasar.

“Bayan tattaunawa da jagororin kungiyar masu kafofin yada labarai da kuma sauran masu ruwa da tsaki a bangaren, mun dauki matakin dakatar da bukatar rufe wasu gidajen labaran a fadin kasar.” in ji Ilelah.

Latest stories

Related stories