Saurari premier Radio
41.6 C
Kano
Wednesday, May 1, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu ya tafka kuskure da ya zabi Musulmi mataimaki-Babachir

Tinubu ya tafka kuskure da ya zabi Musulmi mataimaki-Babachir

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal, ya ce Bulo Ahmad Tinubu ya tafka babban kuskure wajen zabar musulmi a matsayin mataimakinsa.

Wanan na kunshe cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ga manema labarai.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Lahadi ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa 2023.

Lawal ya ce zaben na Shettima ya nuna cewa wasu ‘yan baranda kuma ‘yan amshin-shata ne suka takura Tinubun ya yi haka.

Ya ce bisa ga dukkan alamu, gwamnonin arewa da wasu manyan arewar ne suka sa hakan , da cewa ba za su taba zabar dan takarar da ke da mataimaki Kirista dan arewa ba, kuma shi Tinubun ya yarda da su, in ji Babachir.

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories