Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciBikin Sallah: Yadda kaji ke kanshin dan goma a Kano

Bikin Sallah: Yadda kaji ke kanshin dan goma a Kano

Date:

Hafsat  Bello Bahara

Yayin da ake tunkarar bukukuwan Sallah Karama masu siyar da kaji a  Kano sunce babu ciniki idan aka kwatanta da lokutan Sallah a baya.

Daga cikinsu akwai wadanda suka ce mawuyacin halin rayuwa ne da ake ciki a kasar nan yasa cinikin kajin bai kai na bara ba.

Bisa al’ada a duk lokacin da bikin sallah ya karato a’lummar musulmi kanyi kokarin yin girki na musamman domin shagulgulan sallah cikin annashuwa.

A irin wanann Lokaci na Sallah galibin magidanta kanyi cefane na musamman musamman ma kaji domin a bararraka a yi bikin Sallah.

Hakan kan sa kasuwar kaji ta bude, su kuma samu  ciniki sama da yanda sukeyi a baya.

Toh saide a wannan shekara masu kaji da dama sun koka da halin da suka samu kansu.

Daya daga cikin masu kajin Alhaji Ibrahim Bello Dambatta ya ce  sunyi gagarumar asara a wannan shekarar domin kaji da dama sun mutu saboda yanayin tsananin zafi da aka samu kai.

Haka zalika karuwar farashin abincin kaji ya sanya dole su kara farashin kajin domin su maida kudinsu.

Ahalin yanzu kazar da ake siyarwa Naira 1500 ta karu zuwa Naira 2500.

Ta bangaren al’umma kuwa, sunce matsin rayuwa da ake ciki da kuma hauhawar farashin kajin yasa muradin cin kazar sallah a bana ke dusashewa.

A cewarsu bana dai sai dai  su jiyo kamshi a makwabta, domin basu da halin sayen kazar miyar kamar yanda aka saba.

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...