Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHadarin mota: Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya

Hadarin mota: Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya

Date:

Tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da bayan biyo bayan hadarin mota da ya rutsa da shi a Abuja.

Hadarin ya faru ne ranar Laraba a kan hanyarsa ta komawa gida daga Filin Jirgin saman Abuja zuwa gidansa.

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane biyu cikin hadimansa.

Duk da dai ba a kwantar da shi a kowanne asibiti ba amma dai hadimansan da dama sun samu munanan raunuka.

Rahotannin sun tabbatar da cewa Goodluck din ya dawo ne daga Wani aikin kasa da yaje yi a kasashen ketare

Tuni dai hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC ta tabbatar da faruwar al’amarin.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...