Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan Kwankwasiyya sun mamaye babban zaben NNPP a Kano

Yan Kwankwasiyya sun mamaye babban zaben NNPP a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Dubban yan Kwankwasiyya ne suka mamaye harabar wurin da Jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari za ta gudanar da baban zabenta.

An dai tsara gudanar da zaben ne a cibiyar koyar da Sana’o’i ta sani Abacha wato Abacha Youth Center da ke kan hayar Madobi.

Ana sa ran Jam’iyyar za ta zabi shugabaninta a mataki daban daban ayau Litinin.

Sai dai abinda ke jan hankali a wurin taron shi ne yadda magoya bayan Kwankwasiyya suka mamaye wurin.

Wannan dai baya rasa nasaba da yadda ake ta rade-radin jagoran Kwnkwasiyyar Rabiu Musa zai koma cikin Jam’iyyar.

Idan za a iya tunawa dai tun a watan da ya gabata ne Jam’iyyar ta rushe shugabancinta, tare da kafa kwamitin riko.

A yau Litinin ne dai aka tsara gudanar da zaben shugabannin Jam’iyyar da kuma ake ganin yan Kwnkwasiyya ne suka mamaye dukkanin mukaman da za zaba.

Latest stories

Related stories