Saurari premier Radio
41.6 C
Kano
Wednesday, May 1, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ya baiwa jama'a hakuri kan matsalar mai da lantarki

Buhari ya baiwa jama’a hakuri kan matsalar mai da lantarki

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya nemi gafarar al’ummar kasar nan kan yadda Karancin man fetur ke dagula ratuwarsu.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in yada labaran shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar.

Garba Shehu ya ce tsawon shekara bakwai ke nan gwamnatin Buhari na shawo kan matsalar, in ban da a bana da lamarin ke neman ya ci tura.

“Gwamnatinmu na sane da yadda wahalar man nan ta jefa rayuwar ’yan Najeriya da dama cikin kunci, amma tallafi na tafe nan ba da jimawa ba. Ina baku hakuri a kan haka.

“Muna aiki ba dare ba rana wajen shawo kan matsalar. Akwai ma wani yunkuri da muka fara yi a farkon wannan watan don magance ta.

“Muna aiki tare da Kungiyar Manyan Dillalan Mai ta Kasa (MOMAN) da takwararta ta IPMAN, kuma da alama kwalliya na biyan kudin sabulu.

“An fara samun isasshen mai a wasu jihohin, kuma tuni layi ya fara raguwa a gidajen mai. Ku sa ran ganin hakan a dukkan ragowar jihohin nan da ’yan kwanaki masu zuwa,” inji shi.

Shugaban ya kuma ce ya samu bayanin yadda wasu ’yan kasuwar da masu gidajen mai ke kokarin yin zagon kasa ga yunkurin.

Buhari ya ce tuni ya umarci Ma’aikatar Man Fetur ta Kasa da kamfanin NNPC da sauran hukumomi da su dauki tsattsauran mataki a kan duk mai hannu a lamarin.

Game da batun matsalar wutar lantarki kuwa, Shugaban ya ce ita ma saura kiris a shawo kanta

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...