Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRIKICIN APC: Mai Mala ya rushe shugabancin da Sani Bello ya kafa

RIKICIN APC: Mai Mala ya rushe shugabancin da Sani Bello ya kafa

Date:

Shugaban riko na Jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya yi watsi da sunayen da Abubakar Sani Bello ya fitar da za su gudanar da zaben Jam’iyyar.

Haka kuma Mai Mala ya cire sauran mambobin kwamitin rikon Jam’iyyar watau NEC, dukkaninsu Inda ya ayyana shi Kansa da Sanata John James a matsayin shugaba da sakatare.

Hakama ya cire Minista Lai Moh dungurungun daga Mataimakin Shugaba na Publicity Committee ya sa Fani Kayode a gurbin sa.

Idan za a iya tunawa dai tun bayan da Buni ya tafi asibiti neman lafiya ne Abubakar Sani Bello ya karbi shugabancin rikon Jam’iyyar a inda shi da su Gwamna elRufai suka nemi tsige Mai Maka Buni kuma suka rushe kwamitoci da ya kafa kafin ya tafi.

Alokacin rikon na Gwamna Sani Bello ne ya rantsar da yan kwamitin shirya zabe kimanin guda 20.

Sai dai a jiya Laraba bayan da shugaban kasa ya aikewa zauren gwamnonin APC wasikar da ke neman su sulhunta kansu Buni ya rushe duka kwamitocin kuma ya dawo da nasa da ya kafa da

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories