33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiYan bindiga sun kashe DPO da wasu jami'ai shida a Neja

Yan bindiga sun kashe DPO da wasu jami’ai shida a Neja

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Yan bindiga a jihar Neja sun kashe Wani DPO na ofishin yan sanda na Nasco CSP Umaru Muhammad Dakin Gari.

Haka kuma sun hallaka wasu yan sanda shida tare da DOP.
Rahotanni sunyi nuni da cewa wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin karfe 1.00 na ranar Talata, yayin da ’yan bindigar suka kai sabon hari garin Nasko da ke karkashin Karamar Hukumar ta Magami.

Hakan ce ta sanya wasu jami’an hadin gwiwa da ke jiran ko ta kwana da suka hada da ’yan sanda, dakarun soji da ’yan sa-kai suka tunkare su.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce cikin wadanda suka mutu har da DPO daya, jami’an ’yan sanda biyu da kuma wasu ’yan sa-kai hutu a yayin ba-ta-kashi da ’yan bindigar.

A cewar Abiodun, tuni Kwamandan yankin Kontagora ya tura karin jami’an tsaro yankin domin kwantar da tarzoma da abin da ka iya zuwa ya komo.

Kazalika, ya ce rundunar ’yan sandan jihar ta jajanta wa iyalan jami’an da suka rasa rayukansu, yana mai tabbatar wa da al’ummar jihar cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kawo karshen ta’addancin ’yan bindiga a jihar.

Latest stories