Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIdan PDP ta fadi zabe ta gama yawo-Atiku Abubakar

Idan PDP ta fadi zabe ta gama yawo-Atiku Abubakar

Date:

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce idan jam’iyyar PDP ta fadi zaɓe a 2023, ba za ta iya jure wa adawa har ta tsawon shekara takwas ba.

Atiku ya bayyana haka ne a yau Talata a yayin wani taron tattaunawa da Majalisar Amintattau ta PDP, BoT, a Abuja.

Ya yi kira gare su da su yi aiki tare da shi don cin zaɓen 2023 tun kafin lokacin da za su yi ritaya daga siyasa ya yi.

Ya ce gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Olesegun Obasanjo, wadda ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasa ita ce gwamnati mafi kyau tun 1999.

“Da yawanku kun taka rawa a nasarar gwamnatin PDP daga 1999 zuwa 2006. Babu wata gwamnati da ta cim ma nasarori kamar gwamnatinmu.

“Abin da nake cewa akan gaskiya ne, ku ɗauki kowane ɓangare na ci gabanmu ko tattalin arziƙi, ko lafiya ko fannin noma, ko fannin ilimi, nasarar da muka ci daga 1999 zuwa 2007 ba wata gwamnati da ta cim ma haka.

“Ina cikin damuwa kuma ya kamata ku shiga cikin damuwa cewa idan ba mu ci zaɓe ba, hakan na nufin za mu ci gaba da adawa tsawon shekaru takwas. Daga nan zuwa shekara takwas, ban san mutum nawa ne a cikin za su rage a siyasa ba, kuma hakan zai haifar da mutuwar jam’iyyar”, in ji Atiku.

Game da tsarin karɓa-karɓa, Atiku ya ce bai kamata PDP ta yi haka ba saboda APC ta yi haka.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...