Jam’iyyar APC ta fara sayar da form ga masu sha’awar tsayawa takarar shugabancinta a matakai daban daban.
Jam’iyyar ta sanya Naira Milyan 20 ga dukkanin mai neman takarar shugabancin Jam’iyyar.
Haka kuma Mai neman kujerar mataimakin shugaba zai biya Naira Milyan 10.
Haka kuma Duk mai neman wani mukami da bana shugaba da mataimakinsa na zai biya Naira Milyan 5.
Jami’iyar za kuma ta rufe sayar da Takardar ranar Juma’a mai zuwa, 18 ga Maris 2022