Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMun cikawa ASUU dukkan alkawuran da muka daukar mata-Gwamanti

Mun cikawa ASUU dukkan alkawuran da muka daukar mata-Gwamanti

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce ta biya wa Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU dukkan alkawuran da ta daukar mata a baya don ta janye yajin aikin gargadi da ta tsunduma na makonni hudu

 

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan tsawaita wa’adin yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ta yi da makonni takwas.

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya yi martanin a wata hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Nwajiuba, ya ce gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatun ASUU, inda ya kara da cewa an saki dukkan alawus-alawus da sauran kudaden kungiyar da aka rike.

“ASUU ta kira taro kuma mun amsa gayyata tare da biyan dukkan bukatunsu, ciki har da alawus-alawus da sauran kudadensu amma ba mu san dalilinsu na tsawaita yajin aikin ba,” in ji shi.

Idan ba a manta ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na makonni hudu, kan abin da ta kira gazawar gwamnatin tarayya na cika mata alkawuran da ta dauka tun 2009.

Kazalika, ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da yunkurin tilasta wa mambobinta shiga tsarin biyan albashi na bai daya na IPPIS

Latest stories

Related stories