Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBaya ta haihu, kotu ta dakatar da kamo Dan Sarauniya

Baya ta haihu, kotu ta dakatar da kamo Dan Sarauniya

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Kotun dake sauraron karar Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya ta dakatar da umarnin kamoshi da ta bayar a yau litinin.

A yau ne dai Kotu ta janye belin Dan Sarauniya bisa abinda tace ya gaza bayyana a gaban kotu .

Ana dai  zargin Dan Sarauniya da bata sunan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

To sai dai bayan umarnin kotu cikin gaggawa lauyan dake kare wanda ake zargi ya garzaya kotu don meman mafita.

Jim kadan bayan fitowar lauyan daga kotu ne ya shaidawa Premier Radio  cewa kotu ta dakatar da kama Dan Sarauniya.

Barrister Ghazali Datti ya ce tunda fari kotu ta basu karfe 2 ne domin halattar zaman, sai kwatsam suka sami labarin cewa kotu ta zauna da karfe 1, abida yasa suka garzaya kotu domin jin halin da ake ciki.

Barrister Ghazali ya ce rijistaran kotu ne ya fada musu karfe 2 za su halacci kotun, kuma ya maimaita wannan magana a gaban alkali, hakan kuma yasa alkali ya dakatar da umarnin kama shi.

“Alhamdulillah alkali ya dakatar da kaishi gidan yari, hasalima ya sallameshi ya tafi gida”

“Mu kuma yanzu anyimana izini da mu rubuto a rubuce kura-kuran da suka faru kuma mu roki kotu da ta janye wanna umarni na kamu da tayi na wanda muke wakilta” Inji Barrister Ghazali Datti

Lauyan Dan Sarauniya ya ce yanzu mataki na gaba da za su dauka shi ne rubutowa kotu ta janye umarnin kama Injiniya Mu’azu Magaji Dansarauniya.

Latest stories

Related stories