Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar yan tifa za ta kara kudin yashi, dutse, da kasa

Kungiyar yan tifa za ta kara kudin yashi, dutse, da kasa

Date:

Kungiyar ‘yan tifa ta ce za ta kara kudi kan yadda take sayar da yashi da dutse da kuma kasa sakamakon karuwar kudin diesel da suke amfani da shi.

Shugaban kungiyar Ma’amun Ibrahim Takai ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce a baya sunyi nufin tafiya yajin aiki ne kan matsalar, Amma daga baya suka fuskanci gara suyi Karin kudin.

Ya ce a da suna sayan Lita daya ta diesel akan N 200 zuwa 250, Amma yanzu ya Kai N700 kan kowacce Lita.

Haka kuma ya ce akwai wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da suke amfani da su a motocinsu da aka karawa kudi da kusan kaso 400 cikin Dari.

Ya ce Karin farashin zai fara ne nan take.

Hauhawar farashin kayan ginin dai na ci gaba da dagawa jama’a hankali.

A kwanakin baya dai an samu hauhawar farashin siminti, Inda ya tashi daga N3,700 zuwa kusan N5,000

Wannan dai ta sabbaba tsadar bulo da ake ginin da shi, wanda ya tashi daga N140 zuwa N200, a wasu wuraren ma har ya Kai N250.

Yanzu kuma ga Karin farashin yashi da dutse da na kasa, da ko shakka babu zai karawa masu gini shiga Wani hali

Latest stories

Related stories