Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn nada Sanata Ibrahim Ida wazirin Katsina

An nada Sanata Ibrahim Ida wazirin Katsina

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Mai martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman  ya nada Alhaji Ibramim Ida a matsayin sabon wazirin Katsina.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Sarkin Yakin Katsina kuma Sakataren masarautar, Alhaji Bello Mamman Ifo ya fitar ranar Talata.

Sanata Ida ya maye gurbin Alhaji Sani Abubakar Lugga wanda ya yi murabus daga mukamin nasa na Wazirin Katsina a watan jiya.

Sanata Ida shi ne yake rike da sarautar Sardaunan Katsina kafin nadin nasa.

An haifi Sanata Ida a birnin Katsina a shekarar 1949, kuma ya yi karatunsa na boko a Najeriya da Birtaniya da kuma Amurka.

Sabon Wazirin na Katsina ya soma aikin gwamnati da Babban Bankin Najeriya, kuma ya rike mukamai da dama a gwamnati, ciki har da Babban Sakatare na Ma’aikatar Tsaron Najeriya.

Sannan ya wakilci shiyyar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dattawan kasar tsakanin 2007 zuwa 2011.

Sanata Ida yana da mata daya Hajiya Khadija da ‘ya’ya da jikoki da dama.

Latest stories

Related stories