Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan bindiga sun kaiwa mataimakin gwamnan Kebbi hari, jami’an tsaro 16 sun...

‘Yan bindiga sun kaiwa mataimakin gwamnan Kebbi hari, jami’an tsaro 16 sun rasu

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Jami’an tsaro 16. sojoji 15, dan sanda 1, aka hallaka da fararen hular da ba’asan adadinsu ba a wani mummunan hari da yan bindiga suka kaiwa jerin gwanon motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi Kanal Samaila Yonbe mai ritaya.

Wani shedar gani da ido Musa Muhammed ya gayawa jaridar Punch cewar yan bindigar sun kwashe kakin jami’an tsaron tsaron da suka hallaka.

Mataimakin gwaman na kan hanyarsa ne zuwa kauyan Kenya domin kai gaisuwar yan bijilanti 67 da wasu yan bindiga suka hallaka, kuma a tawagarsa akwai kwamandan barikin soji na Zuru.

Musa Mohammed ya ce an kai wanna harin ne da misalin karfe 8 na daren talatar nan.

Rahotanni sunce mataimakin gwamnan ya tsallake rijiya da baya saidai babban jami’in tsaron mataimakin gwamnan SP Nafiu Abubakar na cikin wadanda suka rasa ransa a harin.

Yace an ajiye gawarwakin jami’an tsaron da suka mutu a babban asibitin Sir Yahaya dake birnin Kebbi.

An gaza samun ji daga sakataran yada labaran mataimakin gwamann Abdullahi Yalmo bayan tuntubarsa da akayikan lamarin kuma har yazuwa lokacin hada wannan rahoto ba’a samu ji daga gareshi ba.

Latest stories

Related stories