Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciRamadan:Ba zamu kara farashin kaya ba-BUA

Ramadan:Ba zamu kara farashin kaya ba-BUA

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Abdussamad Isyaku Rabiu, ya yi wa ‘yan Najeriya alƙawarin cewa kamfaninsa ba zai ƙara farashin kayayyakinsa ba a lokacin azumin Ramadan.

Wakilin BUA na Arewacin Najeriya, Muhammadu Adakawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano a lokacin da yake jawabi game da ƙarin farashin da wasu kamfanoni suka yi a kayayyakinsu.

Kamfanin BUA zai ci gaba da siyar da kayayyaki a farashinsu na yanzu a lokacin Ramadan, kamar yadda Adakawa ya faɗa.

Adakawa ya ce a kwanan nan wasu kamfanoni sun ƙara naira N1,500 akan buhun sukari amma ya ce BUA ba zai yi haka ba.

“A bana, Hukumar Gudanarwa ta Rukunin Kamfanonin BUA ta ga yana da muhimmanci ta saurari tare da amsa kiran abokan ciniki cewa kada wannan kamfani ya ƙara farashin kayayyakinsa musamman sukari.

“Saboda haka, Hukumar Gudanarwar ta umarce ni da in sanar da jama’a cewa ba za a ƙara farashin kaya ba a yanzu har ma cikin Ramadan”, in ji shi.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...