Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAlkalai a Kano sun bukaci Ganduje ya biyasu kudin rawani

Alkalai a Kano sun bukaci Ganduje ya biyasu kudin rawani

Date:

Shugaban Kungiyar Alkalan Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Kano mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya roƙi Gwamna Abdullhi Umar Ganduje da ya biya alƙalan jihar nan kuɗin Rawani.

Wannan dai wani ɓangare ne na alawus – alawus da ake biyan Alƙalai a Kano.

Sarki Yola wanda shi ne alkalin babbar kotun shari’ar Musulunci da ke ƙofar Kudu a birnin Kano, ya ce alƙalai ba kamar sauran ma’aikata ba ne yana da kyau a riƙa kyautatu musu, wajen ganin an sauke nauyin biyansu haƙƙoƙinsu.

Ya kuma roƙi Gwamnan da ya biya su kuɗin Rawani na shekarar da ta gabata, domin karfafawa alƙalan gwiwa wajen gudanar da ayyukansu,

Ya ce akwai bukatar gwamnan  ya dubi ɓangaren su kasancewar ya yi umarni a biya su amma har yanzu kudin bai zo hannunsu

Latest stories

Related stories