Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYajin aikin ASUU: Dalibai na zanga-zanga a Kano

Yajin aikin ASUU: Dalibai na zanga-zanga a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Ɗalibai a Kano sun fito zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu kan yajin aikin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke yike.

Sun fara tattakin ne daga karkashin gadar kofar Nasarawa, sannan suka shiga gidan Murtala don isar da sakonsu ga Kwamishiniyar da ke kula da manyan makarantu.

An samar da jami’an tsaro na DSS da ƴan Sanda daga ƙofar Nasarawa zuwa dukkan mahaɗa ta zuwa gidan gwamnatin Kano, da karkashin gadar Nasarawa.

Tun a makon jiya ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa NANS ta ce za ta ƙaddamar da zanga-zanga a manyan biranen kasar nan kan yajin aikin ASUU.

Latest stories

Related stories