Jam’iyyar APC ta sanar da ranar 23 ga watan mayun nan a matsayin ranar da zata gudanar da zaben fidda gwani na shugaban ƙasa.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Felix Morka ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Larabar data gabata.
Ya ce rahoton da ake yadawa cewa jam’iyyar ta sauya lokutan gudanar da zabukan fidda gwani ba gaskiya bane.
Felix Morka, ya ce za ayi zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar tarayya ranar 15 ga watan Mayu sai na Sanatoci ranar 18 ga watan mayu yayin da da za’a gudanar da na ‘yan majalisar jiha a ranar 20 ga watan Mayu.
Ya kara da cewa za ayi zaben cikin gida na gwamnoni a ranar 21 ga watan nan.
Zuwa yanzu dai kwamitin jami’iyyar APC ya tantance yan takarar da suka haɗa da na Kano Abba Kabir Yusuf da na Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da na Kebbi Nasir Idris da sauran su..
