Al’ummar garin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo na ci gaba da zaman ɗar-ɗar sakamakon sabon harin da aka kai musu a yammacin ranar Alhamis ɗin nan.
Rahotanni sun ce harin ya sake tayar da hankalin mazauna yankin, musamman duba da yadda hare-haren ke ci gaba da faruwa a yankin cikin kwanakin nan.
Idan za a iya tunawa, a makon da muka yi bankwana da shi ma an kai makamancin wannan hari a unguwar Gatarin Fulani da ke garin dagacin Nasarawa, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba tare da ƙara kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro kan sabon harin ba.
