
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shirin bunkasa ilimin ‘ya’ya mata na bankin duniya da hadin gwiwar gwamnatin Kano (AGILE) zai dauki dalibai kimanin dubu 50 a kanannan hukumomi 44 na jihar Kano.
Shugabar bangaren dama ta biyu na shirin (AGILE) Hafsat Aminu Adahama ce ta bayyana haka yayin taron tattaunawa kan cigaban da aka samu a zango na farko da hanyoyin bunkasa shirin a zango na 2.
Hafsat Adhama ta ce zasu fara koyar da daliban da suka dauka sana’o’In dogaro da kai da basu shaidar kammalawa.

A nasa bangaren shugaban sashen kula da tallafawa yara mata da kudi kan harkokin karatunsu, Naziru Surajo, ya ce shirin (Agile) ya samar da kwamfuta 2,500 da solar da kayan aikinta ga dalibai da makarantu da dama a jihar Kano.
Naziru Surajo, ya ce akwai shirye-shirye na cigaba da shirin AGILE yake dada fito dasu domin inganta ilimin ‘ya’ya mata a jihar Kano.
Taron ya samu halartar masana da kungiyoyi na cigaban ilimi da mata daga bangarori daban-daban na jihar Kano.
