Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dan majalisa mai ci Dr Ghali Tijjani Mustapha a matsayin dan takarar maslaha na majalisar tarayya ta Gaya/Ajingi da Albasu, bayan da babban mai neman takarar, Abdullahi Mahmud Gaya ya janye masa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron sulhun ta ‘yan takarar biyu a fadar gwamnatin Kano, wanda hakan ya kawo ƙarshen rade-radin cewa ba za’a cimma maslaha ba a takarar kujerar tarayyar ta Gaya/Ajingi da Albasu.
Da yake tsokaci a yayin sulhun, mataimakin gwamnan Kano Alhaji Murtala Sule Garo, ya ce anfaro aikin sasanci ne tun daga Abuja inda a can din Abdullahi Mahmud Gaya ya nemi a bashi dama ya tattauna da mauksantan sa kafin yanke hukunci.
Shi ma a nasa jawabin yayin sulhun Dr Ghali Tijjani Mustapha ya yabawa Abdullahi Mahmud Gaya bisa janyewa daga takarar, tare da alƙawarin tafiya da kowa da kuma kaucewa duk wani hali da bai dace ba.
A nasa bangaren, Abdullahi Mahmud Gaya ya ce ya janye daga takarar ne domin samar da haɗin kai da ci gaban yankin su da jihar Kano baki ɗaya bayan tuntubar masu ruwa da tsaki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Shugaban jam’iyyar APC na Kano Umar Haruna Doguwa, ya yabawa gwamna Abba bisa ƙoƙarin samar da matsaya ta maslaha a takarar.
