Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƘaruwar Ayyukan Masu Garkuwa Da Mutane Ya Janyo Shirin Sauya Wa Makarantu...

Ƙaruwar Ayyukan Masu Garkuwa Da Mutane Ya Janyo Shirin Sauya Wa Makarantu 359 Matsuguni A Kaduna.

Date:

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sauya wa makarantu 359 matsuguni saboda ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane suna neman kudin fansa.

Gwamna jihar, Uba Sani ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki.

Ya ce ayyukan ƴan bindiga kamar satar ɗalibai a Kuriga da wasu makarantu da ke faɗin jihar na dagula al’amura a ɓangaren ilimi, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Ya ce a dalilin haka ne yanzu haka gwamnati ta fara shirin sauya wa makarantu 359 matsuguni zuwa wasu wuraren da babu matsalar tsaro.

Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da hare-hare na ƴanbindiga waɗanda ke kashewa tare kuma da satar mutane domin neman kuɗin fansa a arewa maso yammacin Najeriya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...