Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiEFCC Ta Kama Mutum 29 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Intanet a Abuja.

EFCC Ta Kama Mutum 29 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Intanet a Abuja.

Date:

Jami’an Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC sun ce sun kama mutum 29 da ake zargi da damfara ta intanet a babban birnin tarayya a Abuja.

Hukumar EFCCn ce ta bayyana hakan a shafinta na X.

Hukumar ta ce an kama su ne a unguwar Apo da Gwarimpa da Katampe da ke Abuja sakamakon samun bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na damfara ta intanet.

Kayayyakin da aka kama daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyi 43 na kera daban-daban da motoci shida da agogo mai kaifin basira guda biyu.

Wani labarin da BBC ta wallafa ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Latest stories

Related stories