Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da ware wa ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai gurbin mutane 50 a auren gata da za a sake yi a jihar.
Daurawa ya ce shirin na da nufin karfafa alaka a tsakanin ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Sheikh Daurawa ya bayyana nasarar da hukumar ta yi a baya, na aurar da mutane 1,800.
Hakan ne ya sa shugaban na Hisbah ya ce hukumar ta yanke shawarar fadada shirin zuwa fannoni daban-daban kamar aikin jarida, doka, da kiwon lafiya.
Sai dai Daurawa bai sanar da ranar da za a fara shirin kashi na biyu na auren gatan ba.