Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar AMAC/Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja Chinedu Obika, ya bada labarin yadda wani ɗan majalisa ya kasa samun kuɗin biyan kuɗin makarantar ‘yarsa har naira 700,000 watanni biyu da suka gabata.
Obika ya ce shi ne ya taimaka wa ɗan majalisar wajen biyan kuɗin makarantar, yana mai cewa lamarin ya nuna ba dukkan ‘yan majalisar ne ke rayuwa cikin yalwa kamar yadda jama’a ke zato ba.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin KAA Truths, yayin da yake mayar da martani kan muhawarar cewa ‘yan Majalisar tarayya na karɓar albashi da alawus masu yawa fiye da kima.
A cewarsa, wannan misali ya ƙaryata zargin cewa dukkan ‘yan majalisar na cin gajiyar abin da ake alakanta da tara dukiya ta hanyar riƙe muƙamin majalisa.
Obika ya ce akwai ‘yan majalisar da ke fuskantar ƙalubalen kuɗi kamar sauran ‘yan Najeriya, duk da matsayin da suke riƙe da shi.
