Jami’iyyar NDC ta karyata wasu labarai da ake yadawa a kafafan sada zumunta kan cewa tana da wasu shari’u a gaban kotu a yanzu haka.
Mai magana da yawun jami’iyyar NDC na kasa Alhaji Ibrahim Ahmad Waya ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Premier radio.
Yace a baya jam’iyyar ta fuskanci kalubalan kan logon jami’iyyar wanda kuma tuni aka kawo karshen matsalar baki dayan ta.
Alhaji Ibrahim Ahmad Waya ya kara da cewa, babu wani rikici da yake damun jami’iyyar NDC a wannan lokacin.
Jam’iyyar ta nuna kwarin gwiwar ta na samun nasarar cin zaban shekarar 2027 mai zuwa.
