Wasu da ake zargin barayin shanu ne sun sake kai wani sabon hari garin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a nan Kano a yammacin Asabar din nan, a dai dai lokacin da mutanan garin suke daf da fara sallar Magriba.
Dagacin garin Lakwaya, Idris Adamu Danbarugu, ya shaida wa wakilinmu Sufyan Halilu Getso ta wayar tarho cewa, maharan sun shiga garin ne ta ƙofar fada, inda suka yi awon gaba da wasu shanu kafin daga bisani su nufi yankin Rugoji.
Ya ce an bashi labarin cewa mutane biyu sun samu raunukan harbin bindiga, sakamakon harin da yan bindigar suka kai.
Idris Adamu ya kara da cewa, jami’an tsaro ba su isa cikin garin ba, sai dai ya ce an sanar da shi cewa sun bi hanyar da ake zargin maharan sun dosa bayan sun kai hari garin na Lakwaya.
Wannan sabon harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu hare-hare makamantan irin wannan, lamarin da ke kara jefa mazauna yankin cikin fargaba da rashin tabbas kan halin tsaro a yankin.
