33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAddiniWani babban Kwastam ya yanke jiki ya mutu a Filin jirgin saman...

Wani babban Kwastam ya yanke jiki ya mutu a Filin jirgin saman Kano

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Wani kwanturola hukumar Kwastam mai kula da Kasuwanci Anthony Ayalogu, ya rasu yana tsaka da aiki a Filin jirgin Saman Malam Aminu Kano.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar AA Mai Wada ya fitar ranar Talata.

 

Ya ce Ayalogu ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi, jim kadan bayan saukarsa a filin jirgin domin gudanar da aiki.

 

Tuni dai aka garzaya da shi Asibitin Rundunar Sojin Saman Najeriya, amma duk da haka rai ya yi halinsa.

 

“Duk kokarin da likitoci suka yi na farfado da shi ya gagara.

 

“Da misalin karfe 8.20 na dare ranar 17 ga Oktoba, 2022, aka sanar cewa ya rasu.

 

“Ya rasu yana da shekaru 57 a Asibitin Runduna ta 465 ta Sojin ta Najeriya da ke Kano.” Acewar Mai Wada.

 

Tuni dai shugaban hukumar na kasa, Hameed Ali, ya jajanta wa iyalan mamacin.

 

Ali ya ce ba shakka Najeriya ta yi babban rashin hazikin ma’aikaci mai kaunar kasa.

 

Kwanturola Anthony Ayalogu, dan asalin Karamar Hukumar Onitsha ta Arewa ne a Jihar Anambra, ya fara aikin kwastam a ranar 24 ga Satumba, 1991, a matsayin Mataimakin Karamin Hafsa (CAS

Latest stories